3 Mayu 2021 - 13:35
Vienna : Za'a Dage Wa Iran Takunkumi A Wasu Bangarori

Wakilai dake tattaunawa game da farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran, sun dakatar da tattaunawar har zuwa ranar Juma’a, inda ake sa ran bayyana abunda aka dadale yayin tattaunawar.

ABNA24 : Kawo lokacin dai an cimma matsaya kan dage wa Iran, takunkumi a wasu bangarori.

Baya ga haka Iran, na mai bukatar a dage mata takunkumi a bangaren makamashi, kere kere motoci, inshore da kuma tashohin jiragen ruwa, da kuma wasu daidaikun mutane da hukumomi.

Karamin ministan harkokin waje, kana mai jagorantar tawagar Iran a tattauanwar, Abbas Araghchi, ya ce an shiga wani mataki na rubata ababen da aka cimma a yarjejeniyar.

Ya ce an kai wani mataki inda aka samu daidaito a bangarori daban daban, an samu daidaito a wasu fanonin kamar yadda ke akwai sabani, a wasu bangarorin inji shi.

Sabani game da batun bukiliya da kuma takunkumai su ne dai ake da sabani a game da su.

Ya kuma ce duk akwai ci gaba a tattaunawar amma ba za’a bayyana cewa ba ga takamaimai lokacin da zamu cimma yarjejeniya, saboda ko wane bangare yana da shi bukatu.

342/